Connect with us

Published

on

Makomar Calvert-Lewin, Gundogan, Lingard, Umtiti, Oxlade-Chamberlain, da Pogba

Rahotanni na cewa Real Madrid na sha’awar dan wasan tsakiya na Manchester City da Jamus Ilkay Gundogan. (Marca)

Ana sa ran dan wasan gaban Everton da Ingila Dominic Calvert-Lewin, ya bar kungiyar a bazara inda aka ce Arsenal da Newcastle United na sonsa. (Football Insider)

Advertisement

Newcastle United na kawar da yuwuwar daukar dan wasan tsakiya na Manchester United Jesse Lingard wanda kwantiraginsa zai kare, har sai dan wasan na Ingila ya rage yawan albashin da yake bukata na fam 150,000 a duk mako. (ESPN)

Mai yuwuwa Arsenal za ta samu aron dan bayan Barcelona da Faransa Samuel Umtiti, (Sport)

Advertisement

A shirye Liverpool take ta saurari tayin sayen Alex Oxlade-Chamberlain, a bazara. (ESPN)

Paul Pogba, zai koma Paris St-Germain ko Juventus idan ya bar Manchester United bayan kwantiraginsa ya kare da bazara. (Eurosport)

Advertisement

West Ham na son rike mai tsaron ragar Paris St-Germain Alphonse Areola. Mai yuwuwa dan Faransar ya sake zaman aro na shekara daya a kungiyar ko kuma ma ta saye shi a kan fam miliyan 11. (Fabrizio Romano)

Newcastle United na son saye dan wasan Aston Villa na baya Matt Targett,wanda ke zaman aro a kungiyar. (Chronicle)

Advertisement

Fulham na son daukar dan bayan West Ham Ryan Fredericks, wanda kwantiraginsa zai kare a matsayin dan wasan farko da kungiyar za ta dauka bayan da ta samu tsallakawa gasar Premier.(Evening Standard)

Watakila mai tsaron ragar Ingila Fraser Forster,ya yi wasansa na karshe ke nan a Southampton saboda kwantiraginsa zai kare a karshen kaka kuma Tottenham na sha’awarsa. (Daily Echo)

Advertisement

Ana sa ran Barcelona za ta sayar da dan bayanta na Sifaniya Oscar Mingueza a bazara, inda kungiyar ke son yuro miliyan biyar a kansa. (Sport)

Tottenham na daya daga cikin kungiyoyin da ke son dan wasan gaba nat Nottingham Forest da Wales Brennan Johnson. (Football.London)

Advertisement

Manchester United za ta saurari tayi a kan dan bayanta Brandon Williams a baara bayan da dan Ingilar ya yi zaman aro a kakar nan a Norwich City. (Manchester Evening News)

Dan wasan tsakiya na Jamus Pascal Gross, da dan gaba na Ingila Danny Welbeck na dab da sanya hannu a kan sabuwar yarjejeniya, a Brighton. (Argus)

Advertisement

Bournemouth ta fasa daukar dan wasan tsakiya na Norwich City Todd Cantwell on a yarjejeniya ta dindindin bayan da dan Ingilar wanda ya yi zaman aro na wata biyar a kungiyar ya taimaka musu suka damar tsallakawa zuwa gasar Premier. (Daily Echo)

Arsenal na shirin sayen dan gaba Marquinhos, dan Brazil mai shekara 19, a kan fam miliyan uku daga Sao Paulo. (Goal)

Advertisement

Dan bayan Manchester United da Portugal Diogo Dalot, yna daga cikin ‘yan wasan da sabon kociyankungiyar Erik ten Hag yake so. (Manchester Evening News)

Swansea City ta yi nisa a tattaunawar sayen golan Arsenal dan Ingila Remy Mitchell, 18. (Football Insider)

Advertisement

EPL results: Man City beat Watford as Chelsea lose to West Ham

Advertisement