Connect with us

Published

on

Mai Bada umarnin Shirin Izzar So Ya Rasu

Nura Mustapha Waye

A yau ne muka samu labarin rasuwar Mai shiryawa Kuma da Bada umarni a shirye shiryen Fina Finan Hausa.

Nura Ya Rasu yau inda akayi janaizar shi a Goron Dutse, inda labari ya karade kafar yada zumunta inda kowa yake ta Mika ta’aziyyarsa da Kuma jimani da Adduar gamawa lafiya.

Advertisement

Ya kasance Daya daga cikin kwararru a fannin Bada umarni da Kuma rubuta labari a masana’antar shirya Fina Finan Hausa na Kannywood.

Sunansa ya fito fili ne bayan fara Shirin Izzar so shiri mai dog zango da ake gabatarwa a YouTube channel ta Bakori TV da Kuma wasu gidajen TV kamar DSTV.

Advertisement

Afritechzone da ma’aikatanta gaba Daya na sakon ta’aziyyarmu ga iyalanshi, Yan uwa da abokan Arziki.

Allah ya gafarta masa Kuma yasa muyi karshe me kyau.

Advertisement