Connect with us

Published

on

Mahadin Bam ne Suka Haddasa Fashewa a Sabon Gari Kano

Bomb blast Sabon gari

Rundunar ‘yan-sandan Najeriya a jihar kano ta ce fashewar da ta auku a wani shago a unguwar Sabon Gari da ke jihar a ranar Alhamis 17 ga watan Mayu, wadda ta hallaka mutum tara (9) ta faru ne a sanadiyyar wasu sinadarai da ake iya hada bam da su.

A lokacin da fashewar ta auku an rika yada labari masu karo da juna dangane da musabbabin abin, inda wasu ke cewa bam ne ya tashi wasu kuma ke cewa tukunyar gas ce ta mai aikin walda ta fashe a shagon.

Advertisement

A tattaunawarsa da wakilinmu a wurin da fashewar ta auku, a ranar, kwamishinan ‘yan-sanda na jihar ta Kano CP Sama’ila Dikko ya ce tukunyar gas da ake walda da ita a wajen ce ta fashe, “amma ba bam ne ya tashi ba kamar yadda ake faɗa,” in ji Kwamishinan.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2022, rundunar ta ce mutumin da yake gudanar da haramtaccen kasuwancin na sayar da wadannan haramtattun sinadarai, wadanda ake hada bam da su, da aka gano, Michael Adejo, ya mutu a fashewar.

Advertisement

Sanarwar ta ce, ”Binciken farko-farko ya nuna cewa daga cikin mutum tara da fashewar ta rutsa da su, daya daga cikinsu yana ajiye sinadarai masu lahani da sauran abubuwa masu hadari ba bisa ka’ida ba mai suna Michael Adejo, (wanda ya mutu).”

Rundunar ‘yan-sandan a wannan sanarwa ta ranar Asabar ta tabbatar da mutuwar mutum tara da kuma wasu takwas wadanda suka hada da dalibai da ta ce sun samu ‘yan raunuka a sanadiyyar fashewar ta ranar Talata.

Advertisement

‘Yan-sandan sun bayyana sunayen wadanda suku mutum kamar haka, Ejike Vincent (mai walda) da Michael Adejo (mai sayar da sinadarai) da Musa Kalla (mai sayar da shayi da Christiana Abosade da Mary da Austine Dada da Madam Owoleke da Omo Ben da kuma Bose Oladapo.

Sabon Gari

Rundunar ta kuma bayyana wasu tarin durum-durum da jarkoki da ke dauke da sinadarai iri daban-daban, masu hadari da ta ce ta gano a inda lamarin ya faru.

Advertisement

Ta ce binciken kwararrunta a kan bam, ya nuna cewa suna zargin fashewar ta auku ne a sakamakon haduwar wasu sinadari da wuta.

A sanarwar, rundunar ta kuma ce ta yi kame na wasu da ke da alaka da daya daga cikin shagunan da suka rushe a fashewar, wanda ake haramtaccen kasuwancin sayar da sinadarn da ababan da take zargi ana hada bam da su. Ta kuma samu shedar sayen kayayyakin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Advertisement

Tinubu da Shekarau: Abubuwan da manyan ‘yan siyasar suka tattauna

Fashewar wadda ta auku a gida mai lamba 01 kan titin Aba/Court Road a unguwar Sabon Gari ya yi sanadiyyar rushewar gidan, wanda yake da shaguna hudu a kasa da kuma bene. Akwai kuma wata makarantar boko ta yara, Winner Kids Academy a tsallaken gidan, inda da farko aka rika cewa a makarantar ne aka tayar da bam.

Advertisement

 

Advertisement