Connect with us

Published

on

Kwamishinonin Ganduje Sun Ajje Aiki Don Neman Takara 2023

Gwamnatin Kano

Masu muƙaman siyasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya na ci gaba da ajiye mukamansu saboda sha’awar fitowa takara a zaben 2023.

Hakan na zuwa ne bayan umarnin da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayar ga masu sha’awar tsayawa takarar a kan su sauka daga duk wani mukami na gwamnati.

Advertisement

Wani ɗan jarida da ke gabatar da shirye-shiryen siyasa a jihar ta Kano, Bashir Sarki, ya shaida wa wakilinmu cewa kawo yanzu kusan mutum tara sun ajiye mukamansu tun bayan umarnin gwamnan.

Ya ce cikin waɗanda suka ajiye aiki zuwa yanzu, har da Nasiru Yusuf Gawuna, mataimakin gwamnan Kano wanda ya sauka daga matsayin Kwamishinan Noma; da Murtala Sule Garo, Kwamishinan Kananan Hukumomi, da na Raya Karkara, Musa Iliyasu Kwankwaso.

Advertisement

Akwai kuma Nura Muhammad Dankade, Kwamishinan Kasafi da Kwamishinan Ilimi, Sunusi Sa’idu Kiru.

Bashir Sarki ya ce yawanci ajiye aikin nasu ba ya rasa nasaba da aniyarsu ta tsayawa takara da kuma la’akari da sashen da ake ta dambarwa a kansa na cikin sabuwar dokar zabe ta 2022 da ya bukaci masu neman mukamin siyasa su ajiye aikinsu idan suna da sha’awar yin takara tun yanzu.

Advertisement

Dan jaridar ya ce “Wasu daga cikin waɗanda suka ajiye muƙaman nasu ana kyautata zaton za su fito takarar gwamna, sai kuma wasu da ake ganin za su fito takarar Majalisar tarayya da masu neman majalisar jiha.”

Ya ce a ranar Asabar 16 ga watan Afrilu na 2022, ne gwamnan jihar ta Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da sanarwa cewa duk mai rike da mukamin gwamnati ya ajiye mukamin zuwa ranar Litinin 18 ga watan na Afrilu.

Advertisement

Bashir Sarki ya ce sanarwar gwamnan ta zo a ƙurarren lokaci, domin haka ba mamaki wasu daga cikinsu za su haƙura da aniyar tsayawa takara baki ɗaya idan ba su samu damar ajiye aiki kafin karewar wa’adin da gwamnan ya bayar ba.

Za mu soke ƴan takarar jam’iyun da ba su yi zaɓen fidda-gwani nan da wata 1 — INEC

Advertisement

Ya ce “Akwai wadanda kuma suna da sha’awar tsayawa takara amma har yanzu ba su sauka ba, kamar shugaban hukumar Karota, Baffa Babba Dan Agundi, wanda ake tunanin zai kara komawa ya nemi takarar dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Birni da kewaye, akwai kuma kwamshinan matasa da wasanni, Kwamared Ado Lakwaya, wanda ake ganin zai nemi takarar dan majalisar tarayya daga yankin Kabo da Gwarzo.”

”Sauran sun hada da kwamishinan lafiya, Dakta Tsanyawa, shi ma ana ganin kamar zai nemi takarar majalisar tarayya a yankin Kunchi da Tsanyawa, akwai kuma Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba, shi ma ana ganin zai nemi takarar majalisar tarayya a yankin karamar hukumar Birni da Kewaye, to amma shi ba ya nan, ya je Umrah” in ji Bashir.

Advertisement

Ya ce ba mamaki cikin makon da za a shiga gwamnan ya bayar da sanarwa a kan wadanda za su maye gurbin wadanda suka yi murabus din, ko kuma gwamnati ta ce ta bar manyan sakatarorin ma’aikatu da hukumomin da aka samu gibi su ci gaba da tafiyar da al’amura a can.

 

Advertisement
Advertisement