Connect with us

Published

on

Kungiyar Arewa Maso Yamma Masu Fafutukar Kawo Cigaban Najeriya (NEWDEG)

May be an image of 1 person, standing and text

Dalilan da suka Wajabtawa Deliget din PDP yan Arewa Maso Yamma Zaben Alh. Bukola Saraki Don cigaban Arewa da Najeriya baki daya.

Waye Alh. Abubakar Bukola Saraki?

Shidai Sanata Saraki Yasamu gogewar da kasar mu a yanzu take bukata a tattare da shugaba, musamman a wannan lokacin da muke fama da tsananin ta6arbarewar tattalin arziki da rashin tsaro.

1. (a)

Advertisement
Na farko, Alhaji Bukola Saraki mutum ne Wanda ya samu horarwar ilimin likitanci Wanda ya goge a fannin kula da lafiya Dan Adam.

(b) Ya samu ilimin lissafin kasuwanci da tattalin arziki tare da horaswar aikin banki inda ya kai kololuwa a wurin aikin.

(c) Ya samu gogewar sanin tsarin kasafin arzikin kasa inda zai iya samar da daidaito wurin yin adalci ga jihohi wurin rabon arzikin kasar, Wanda hakan zai taimakawa Najeriya wurin samun zaman lafiya.

Yasamu wannan ilimi ne a lokacin da yayiwa tsohon shugaban kasa Chief Obasanjo mataimaki na musamman akan kasafin kudi da tsare tsare (Budget and Planning)

Advertisement
Alh. Bukola Saraki yayi Gwamnan jihar Kwara tsawon shekara Takwas, yayi shugaban gwamnonin Najeiya tsawon shekara hudu (2007-2011) wannan zai taimaka masa wurin yin aiki tare da fahimtar da gwamnoni Don warware matsalolin jihohi.

Alh. Abubakar Bukola Saraki yayi sanata shekara takwas, kuma yayi shugaban majalisar dattijai ta sanatoci, tsawon shekara hudu. Wannan ma zai taimaka masa wurin samun daidaito da hadin kan yan Majalisu Don cinma burin aikin da yake da niyyar yiwa kasar baki daya. Domin rashin hadin kan majalisu da shugaban kasa yana kawo tsaiko da ci baya ga shugaban kasa da yan kasar, da kuma kasar baki dayan ta.

2. Sanata Saraki mutum ne Wanda yafito daga arewa ta tsakiya daga jihar Kwara. Jam’iyyar APC tanada alkawarin cewa idan Shugaba Buhari ya gama wa’adin mulkinsa matsayinsa na Dan Arewa, toh ba makawa yankin kudu musamman yarbawa, su zai mayarwa mulki. Don haka Arewa bata da daman kawo Dan Arewar a matsayin shugaba karkashin Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Advertisement
A dayan bangaren kuma, a Jam’iyyar ta PDP, Dan Arewa maso yamma ne ya taba yin mulkin kasar tun bayan kafuwar jam’iyyar ta PDP. Wato Marigayi Alh. Umaru Musa Yar’adua.

Yanzu daman da Arewa take dashi yana daga Jam’iyyar PDP ne, Kuma daga Arewa ta tsakiya ko Arewa maso Gabas.

Arewa Maso Gabas Sunada yan takarkaru masu karfi Guda Biyu, Mai Girma Alh. Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) da Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Mohammed Bala Abdulkadir. Sai gogaggen Dan kasuwan nan wato Mohammed Hayatuddeen.

Shidai Alh. Atiku Abubakar shekaru sun cinmasa, ya haura shekara 70 a duniya. Munajin tsoron kar irin raunin shekarun da suka sanya Shubaga Buhari ya kasa rike kasar, wannan iftila’in ya kara faruwa damu akanAlh. Atiku Abubakar. Ba shakka Yadda Alh. Atiku Abubakar yake da karfin Hali Da jajircewa da kokari da gogewa, haka Shugaba Muhammadu Buhari yake da irin wannan siffofi masu kyau.

Advertisement
Kash, sedai tsufa shekaru sun hana Shugaba Buhari aiwatar da abinda ya dace, haka zasu iya faruwa da Mai Girma Alh. Atiku Abubakar.

Shi kuwa Mohammed Hayatuddeen yanada yawan shekaru shima, sannan bashi da gogewar siyasar da zai iya gogaiya da yan takarar kudu. A yanzu bazamu iya kasadar mara mishi baya ba. Don kar mu rasa tsuntsu mu rasa tarko.

3. Alh. Abubakar Bukola Saraki ya zama shine daya tilo Dan takara mai karancin shekaru, mai tarin ilimi na fannoni daban daban kamar yadda muka lissafo a sama, shine mai experience din da duk yan takarar da muke dasu yanzu a Arewa babu kamar shi.

Wannan sune dalilai kwarara guda uku da suka wajabtawa Deliget din jam’iyyar PDP na Arewa maso Yamma da Arewacin Najeriya gaba daya, marawa Sanata Abubakar Bukola Saraki baya don ganin yazama sanadiyar da Allah zai ceto arewar daga halin da muke ciki.

Advertisement
A takaice, duk fadin Najeriya, a yan takarar da suka fito neman shugabancin kasar, kusan babu Wanda yake da irin siffofin da Shi Alh. Abubakar Bukola Saraki ya mallaka

Idan Dan mu na Arewa bai iya magance matsalar Arewa ba, toh tabbas Dan kudu sedai ma ya karasa mu in ya samu dama.

Gwara mu samo mutum mai karfi da gogewa mai nagarta mu saka shi a gaba Don ceto yankin mu.

Muna Kira ga deliget dinmu na Arewa ku duba wannan tunani na kwarrarun masana mulki da shugabanci daga cikin mu, domin shawo kan matsalar da ta addabemu a Arewa.

Advertisement
Mu hakura da son rai da son zuciya, muyi abinda zai fish-shemu alkhairi.

Ibrahim Ibrahim Mu’azzam11th May 2022

A Madadin Kungiyar rajin cigaba da tsaron Arewa Maso Yamma (NEWDEG)

Advertisement
Advertisement