Connect with us

Published

on

Ba batun siyasa na tattauna da Bola Tinubu ba – Obasanjo

obasanjo

Tsohon shugaban Kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce ba tattaunawar siyasa suka yi da ɗan takarar shugabanci kasa na APC ba, Bola Ahmed Tinubu.

Obasanjo ya gargadi magoya bayan Bola Tinubu kan yaɗa cewa ya marawa takarar Tinubu baya a ganawar sirri da suka yi a gidansa da ke Abeokuta a ranar Laraba.

Advertisement

Ya ce yaɗa irin wadannan labarai marasa tushe na lahani ga ‘yan siyasa irinsu Tinubu.

A wata sanarwa da maitaimaka ma sa na musamman ya fitar, kehinde Akinyemi, na ambato Obasanjo na cewa ganawarsa da Tinubu ta ‘yan uwantaka ce ba siyasa ba.

Advertisement

Wannan na zuwa ne bayan kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a wani taro na APC a Lagos ya na mai cewa ganawar Obasanjo da Tinubu alamar nasara ce garesu a zaben 2023.

Tsohon shugaba Obasanjo dai ya sake jadada cewa shi uba ne ga duk ‘yan Najeriya da matasa da ke cikin matsi.

Advertisement

Tinubu da Shekarau: Abubuwan da manyan ‘yan siyasar suka tattauna

Advertisement